Babban Kamfanin Koc Holding na Turkiyya na shirin zuba jarin dala biliyan 4 a shekara mai zuwa, ban da saye da sayarwa, in ji shugaban kungiyar Turgay Durak a ranar Alhamis.
Ya ce a wani taron koli na manyan shuwagabannin zartarwa, wannan adadi ya hada da sanannun jarin da kamfanonin tace mai na Tupras, da masu kera motoci Ford Otosan da Tofas da kuma kamfanin kera kayayyakin lantarki na Arcelik.
(Reuters)



